Labarai
Kano: Rundunar Civil Defense ta fara bincike kan zargin jami’anta da karɓar cin hanci
Rundunar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta nesanta kanta da wasu jami’ai da ake alakanta rundunar da su wadanda ake zargin suna karbar cin hanci a daga hannun masu gidajen siyar da man fetur da masu dillancinsa.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar DSC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar da yammacin jiya Lahadi.
Sanarwar ta ce ko kadan ba jami’an rundunar Civil Defense ne ke karbar cin hanci ba kamar yadda aka ankarar da rundunar akan abinda ke faruwa.
Haka kuma, sanarwar ta ce, yanzu haka kwamandan rundunar Adamu Idris Zakari, yabada umarnin kuma an fara gudanar da bincike domin bankado masu aikata irin wannan cin amana domin daukar matakin shari’a a kansu.
DSC Ibrahim ya kuma ce, ”Babu inda Civil Defense ta Kano ta tura jami’anta gurin masu gidajen sayar da man fetur da masu dillancinsa domin su karbi cin hanci da rashawa daga wajen su”.
Rundunar ta yi kira ga mutane da su gaggauta kai mata rahoton masu irin wannan dabi’a.
