Connect with us

Labarai

Da ɗumi-dumi: Jami’an DSS sun ritsa Emefiele a ofishinsa

Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun mamaye shalkwatar babban bankin Najeriya CBN tare da ritsawa da kuma ƙwace iko a ofishin gwamnan babban bankin Godwin Emefiele.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jami’an DSS da Mista Emefiele kan zargin tallafa wa ta’addanci.

Tun a baya hukumar ta buƙaci kotu da ta bata izinin cafke Godwin Emefiele, sai dai gwamnan babban bankin ya fice daga Najeriya domin hutun ƙarshen shekara wanda zai ƙare a gobe Talata.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a watan Disamban da ya gabata ne babbar kotun birnin tarayya Abuja ta haramta wa jami’an DSS kamawa ko tsarewa ko kuma gayyatar Emefiele.

Sai dai, da yammacin yau Litinin jami’an hukumar sun yi kutse cikin babban bankin na CBN cikin motoci kusan ashirin.

Haka kuma ta ruwaito cewa, jami’an sun hana duk ma’aikatan CBN shiga ofishin Mista Godwin Emefiele.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet