Labarai
Wata Gobara Ta Tashi A Wani Gidan Mai Na AA Rano
Wata Gobara ta tashi a wani gidan mai mai suna AA Rano dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Lahadi.
A cewar rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, a cikin wata sanarwa, jami’an ‘yan sanda da jami’an kashe gobara sun isa wurin a kan lokaci domin kashe gobarar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Josephine Adeh, ta ce, “An samu gobara a gidan mai na AA Rano.
Gobarar dai ta tashi ne a lokacin da wata tankar mai ke sauke man a tashar.
“Jami’an ‘yan sanda, ma’aikatan kashe gobara da sauran masu ba da agajin gaggawa sun kasance a wajen don kashe gobarar tare da tabbatar da barnar bata yadu ba ga mutane da dukiyoyi.”
