Connect with us

Featured

Ɗan Majalisar Tarayya A Zaria Ya Maka Wani Ɗan Jarida A Kotu

Daga Nasir G. Fagge

 

Zababben Dan majalisar Tarayya mai wakiltar Zariya Hon Dr Abbass Tajuddeen ya Maka fitaccen matashin dan jaridar nan dake Zariya Saifullahi Lawal Imam a kotu bisa zargin yana so ya bata masa Suna da zubar masa da mutunci.

Dan Majalisar dai ya kai Dan jaridar kotu ne a shekaran jiya Alhamis, jn da kuma za a shiga kotun ranar biyu ga watan fabairun mai zuwa.

A zantawa da aka yi da matashin dan Jaridar akan wannan lamarin, ya bayyana cewa shi bai ma san abunda ake zarginsa da shi ba, domin bai san mai yayi wa dan majalisar ba da har aka kai shi kotu.

Saifullahi Lawal Imam ya kara da cewa “Ni tsohon yaron gidan Dan majalisar Tarayyar ne, tun shekara ta 2015 nake gidansa ina masa hidima, ina kareshi daga abokan adawa da kare masa kima da mutunci, ban taba neman komai a wajensa ba, domin saboda Allah nake ƙaunar sa.

” Al’amarin ya faru ne lokacin da wata cuta ta kamani a kunnena wacce ke barazanar kurumtar dani, inda na bukaci taimakon Dan majalisar wanda na dauka kamar uba a gareni akan taimakamun domin a mun aiki, inda yayi alkawarin zai nemar mun taimako don ganin an mun magani in cigaba da jin magana, amma tsawon lokaci watanni da dama bai taimaka mun ba duk da biyayyata da Sadaukarwata ga siyasar Gidansa”.

“Wanda Sau uku ana kulleni a Caji Offis saboda kare masa mutunci daga abokan adawa, ganin ciwon na cigaba da tsanantawa har gashi na daina jin magana tasa na yanke shawarar barin tafiyar Gidansa Sabili da la’akari da na yi da cewa ba za a taba taimakamun a gidan siyasarsa ba duk da Sadaukarwata a gareshi”.

“Bayan na bar tafiyar gidan nasa na koma gidan babban abokin adawarsa na jam’iyyar Labour Party Wato Hon Suleiman Ibrahim Dabo wakili, A duk rubuce-rubucen da nake na tallata Wakiline amma sai gashi an kawomun Sammaci wai na batawa dan majalisar Tarayya Suna ba tare da na san ta yaya hakan ta faru ba”

Saifullahi Lawal Imam wanda kuma mambane a kungiyar Jaridun kafafen Sadarwa na zamani, kuma Mamba a kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty international da kuma Human Right Network ya danganta lamarin da bita da kulli don ganin bayansa, inda ya bayyana cewa hakan ba zai taba Samun nasara ba..

A na su martanin Kungiyar Yan Jarida ta kasa A wani zama da sukayi jiya a kaduna sun bayyana cewa suna jira ne su ga motsin da dan majalisar zai yi akan mamba na su wato Saifullahi Lawal Imam kafin daukar mataki.

Suma kungiyar Kafafen yada labarai a Dandalin Sadarwar Zamani Arewa Online Journalist Forum sun bayyana wannan lamarin a matsayin abun takaici ga dan majalisar, inda suka bayyana matakin na dan Majalisar a matsayin abun kunyar da ba za a amince da shi ba “Idan yana da matsala da mamban namu ya nemi shugabannin kungiyar mana don Shawo kan lamarin”… Cewar Shugaban kungiyar..

Kana kungiyar ta tabbatar da cewa ba za suyi kasa a gwiwa ba waje ganin hakar dan majalisar Tarayya na wulakanta Dan jaridar bai ci Nasara ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet