Labarai
Hisbah Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Uwar Da Ta Kashe Aurenta Ta Aure Saurayin Diyarta
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan zargin da aka yiwa wata mata bisa kashe aurenta kuma ta aure saurayin yarta a jihar.
Babban kwamandan hukumar Sheikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan da aka yi zargin kwamandan hukumar na karamar hukumar Rano ne ya raba auren matar.
Iyayen matar su ne suka yi korafi kan cewa kwamandan na Rano ya aurar da yarsu ga sairayin yarta ba tare da izininsu ba.
Jaridar Alkiblah ta baku labarin yadda wata Uwa ta kashe aurenta ta kuma yi wuf da sairayin yar ta ta, bisa cewarta bai kamata ita da yarta su yi asarar saurayin ba.
Babban kwamandan na Hisba ya ce kwanaki biyu da suka gabata labarin ya iso tebirinsa cewa wata mata ta kashe aurenta, kuma ta auri saurayin yarta.
Ibn Sina ya ce bayan samun labarin nan take ya kafa kwamitin bincike game da lamarin.
Ya ce tuni suka gayyato duk bangarorin da lamarin ya shafa, kuma yanzu haka bincikensu ya yi nisa.
Haka kuma ya ce da zarar kwamitin ya kammala bincikensa za su sanar da Duniya halin da ake ciki game da lamarin da kuma matsayar hukumar ta Hisbah.
Sheikh Ibn Sina ya ce wannan labarin yana da rikitarwa da basu taba ganin irinsa ba, duk kuwa da cewa suna samun rahotannin matsaloli masu yawa a kowace rana.
