Labarai
Wata sabuwa: Ganduje ya sallami Muhyi daga aiki
Gwmanan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sallami dakataccen shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa PCACC Muhyi Magaji Rimin Gado, daga shugabancin hukumar.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda da sakataren gwamnatin Kano Alhaji Usman Alhaji ya aike wa Muhyi Magaji.
Takardar, ta ce, Gwamna Ganduje ya amince da matsayar da majalisar dokoki ta cimma na cire shi daga mukamin.
Idan za a iya tunawa, a watan Yulin bara negwamnan ya dakatar da Muhyi daga shugabancin hukumar sakamakon wani saɓani da ya shiga tsakaninsu.
