Connect with us

Labarai

Majalisar dokokin Kebbi ta yi sammacin gwamnan jihar

Majalisar dokokin jihar Kebbi, ta gayyaci gwamnan jihar Alhaji Abubakar Atiku Bagudu kan amfani da bashin Naira miliyan dubu 18 da dubu ɗari bakwai daga gwamnatin tarayya.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wasikar da majalisar ta aike wa gwamnan mai kwanan watan 26 ga watan Janairun bana.

Haka kuma ta cikin takardar, majalisar ta buƙaci gwamnan da ya bayyana a gabanta yau Juma’a.

A cewar wasikar hakan ya yi daidai da kokarin da majalisar ta yi na tabbatar da kula da dukiyar jihar cikin tsanaki .

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, wasikar ta kasance kamar haka: Dangane da bukatar ku na amincewa da Gwamnatin Kebbi ta karbo bashin kudi daga gwamnatin tarayya mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021 tare da mai lamba No. GHBK/8/21 Vol.1

‘’ Majalisar Dokokin Jihar Kebbi ta amince da kudi har sama da Naira Miliyan Dubu Goma sha Takwas (18,746, 059,992.57) ta hanyar kudiri mai kwanan wata 18 ga Oktoba, 2021.’’

A ci gaba da kokarin da take yi na kula da albarkatun kasa cikin tsanaki majalisar tana neman Gwamnan da ya gurfana a gaban majalisar domin yin bayani kan yadda za ayi amfani da kudaden a ranar Juma’a 27 ga Janairu, 2023 da karfe 10:00 na safe.

Haka kuma ta bayyana cewa wasiƙar da Suleiman Shamaki, mukaddashin magatakardar majalisar ya sanyawa hannu tana mai take ‘’Re: Offer of Federal Loan Facility’’.

Haka kuma kafar ta ce, an makala wasikar ne tare da sanya hannun ‘yan majalisa 20 daga cikin 24 na majalisar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet