Labarai
Da ɗumi-dumi: CBN ya umarci bankuna su fara bada sababbin kuɗi a kanta
Babban bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan kasuwanci da su fara bai wa mutane sababbin kuɗi da ba su haura Naira dubu Ashirin ba a kan Kanta.
Daraktan sadarwa da yaɗa labarai na babban bankin Osita Nwanisobi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce, babban bankin zai yi haɗin gwiwa da hukumar ‘yan sandan Najeriya da hukumar tattara haraji ta tarayya FIRS da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC da kuma sashen kula da harkokin kudi na Najeriya NFIU, domin hukunta masu masu sayar da sabbin kuɗi a bankuna.
Ta cikin sanarwar dai, Osita Nwanisobi, ya ce, CBN ya lura tare da nuna matuƙar damuwa bisa yadda mutane ke sayar da sabbin takardun kudi da aka yi wa gyaran fuska lamarin da ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.
