Labarai
Kotu ta raba auren Asiya Ganduje da mijinta
Babbar kotun shari’ar musulunci a jihar Kano, ta raba auren ƴar gwamnan Ganduje watau Asiya Abdullahi Umar Ganduje da mijin ta Alhaji Inuwa Uba, ta hanyar yin Khul’i.
Tun da farko dai Asiya ɗin ta hannun lauyanta, ta shigar da ƙara a gaban kotun tana mai buƙatar a raba auren nasu.
Yayin shigar da ƙarar, uwar gida Asiya Ganduje, ta ce za ta mayar wa Alhaji Inuwa Uba, sadakin da ya bata naira dubu hamsin.
Arewa Radio ta ruwaito cewa, yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Malam Abdullahi Halliru, Ya ce hujjojin da aka gabatar a zaman shari’ar sun tabbatar da cewar mai ƙarar ta karɓi naira dubu hamsin ne a matsayin sadaki.
Haka kuma ta ruwaito, cewa, a nasa ɓangaren, Lauyan mijin nata Umar I Umar, Ya yi fatan kotun ta ba shi dukkan bayanai na yadda zaman kotun ya kasance domin yin shirin ɗaukaka ƙara zuwa kotun sama.
