Labarai
Kotu ta bada umarnin tsare Murja Kunya a gidan Yari
Wata Kotu a jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare fitacciyar ƴar TikTok Murja Ibrahim Kunya, a gidan Gyaran Hali.
Kotun ta bada umarnin ne da tsakar ranar yau Alhamis bayan da ta kammala sauraron shari’ar da ake yi wa Murja Ibrahim, inda ta ce a ci gaba da tsare ta zuwa ranar 16 ga wannan watan da muke ciki na Faburairu da za a dawo domin ci gaba da shari’ar.
Ana zargin Murja Ibrahim Kunya, da yin kalaman rashin ɗa a da suka saɓa da tarbiyya har ma zamantakewar musulmi.
Tun farko dai Zauren haɗin kan malaman jihar Kano ne suka yi ƙarar matashiyar da wasu sauran matasa maza da mata a Kotun shari’ar musulunci da ke garin Bichi, inda a cikin makon da muka yi ban kwana da shi ƴan sanda suka cafke ta.
Sai dai, bayan karanta mata tuhume-tuhume Murja Ibrahim ta musanta batun.
