Connect with us

Labarai

El-Rufai Ya Mayar Da Kakkaisan Martani Ga Mutanen Fadar Shugaban Kasa

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ja kunnen ‘yan fadar Aso Rock “cabals” da ya yi imanin cewa suna adawa da burin zama shugaban kasa na Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar jam’iyyar (APC) a zaben shugaban kasa na 2023.

Jaridar Daily Trust El-Rufai dai ya haifar da cece-kuce a ranar Laraba lokacin da ya ce wasu mutane a Aso Rock suna yi wa Tinubu zagon kasa.

Yayin da yake amsa tambaya a wata hira da BBC Hausa wanda har yanzu ba a fitar da cikakken bayani ba, El-Rufai ya ce, “Mutunta mutane ba tsoro ba ne, na rantse ba ma tsoron kowa a kasar nan, don haka ba ma tsoro, muna mutuntawa amma idan ka nuna mana kai ba dattijo ba ne, na rantse za mu yake ka.”

An yi musayar kalaman gwamnan na baya-bayan nan a shafukan sada zumunta kafin cikakken sakin.

El-Rufai ya yi magana ne a fili a martani ga ” mutanenVilla ” da ya yi magana a cikin hirar da gidan talabijin na Channels.

A lokacin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, El-Rufai ya ce mutanen da suka goyi bayan wani dan takara na daban a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a yanzu suna fakewa da shugaba Buhari don biyan bukatunsu.

“Na yi imanin cewa akwai wasu mutane a cikin Villa da ke son mu fadi zabe saboda ba su samu ba; suna da dan takararsu. Dan takararsu bai ci zaben fidda gwani ba. ”

“Suna kokarin ganin mun fadi zabe ne, kuma suna fakewa da burin shugaban kasa na yin abin da yake ganin ya dace,” in ji shi.

Aisha, uwargidan shugaban kasa ta goyi bayan El-Rufa’i kan ikirarin da ya yi cewa wasu daga cikin kusoshin fadar shugaban kasa na shirin yin zagon kasa ga nasarar Tinubu.

Uwargidan shugaban kasa wadda ke da tasiri sosai a fadar ta Villa ta bayyana goyon bayanta ga El-Rufai a lokacin da ta yada wani faifan bidiyon hirar da ke dauke da babban zargin da gwamnan ya yi kan masu zagon kasa wadanda ba ‘ya’yan jam’iyyar ba ne kuma suke amfani da yardar shugaban kasa.

Sai dai ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya mayar da martani yana mai cewa a hukumance gwamnati ba ta da masaniyar wani a cikin fadar shugaban kasa da ke yin irin wannan aiki.

Ya ce gwamnati ta yi adalci ga duk ‘yan takara ba tare da la’akari da jam’iyya ba, kuma Buhari ya nuna cewa ya yi zabe mai inganci da adalci.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet