Siyasa
Kotun ƙoli ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin ƴar takara
Kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari, a matsayin ƴar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a tutar jam’iyyar adawa ta PDP.
Tun a baya dai kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Laila Buhari a matsayin ƴar takarar bayan da ta soke zaɓen Danburan Nuhu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa, a hukuncin da kotun ƙolin ta yanke wanda mai shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, kotun ta yi watsi da dukkan dalilan ɗaukaka karar, da Danburam Nuhu, ya gabatar mata.
Haka kuma kafar ta bayyana cewa, yayin yanke hukuncin, Mai shari’a Garba na tare da Justice Kudirat Kekere Ekun da Justice Saulawa da Justice Ibrahim Jauro, da kuma Justice Emmanuel Agim.
