Labarai
‘Yan Majalisu Za Su Dawo Aiki Kafin Zabe Muddun Yan Najeriya Suka Cigaba Da Wahala – Gbajabiamila
Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce majalisar wakilai za ta koma zama kafin babban zaben kasar idan har wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta kan sabon kudin Naira da aka sauyawa fasali ya ci gaba da kasancewa.
Gbajabiamila, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Lanre Lasisi, ya fitar jiya, a wani taro da ya yi da wasu kabilu a Surulere, Legas.
Ya ce majalisar za ta ci gaba da sanya ido kan yadda babban bankin Kasar ke aiwatar da manufofin.
Ya ce: “Majalisar wakilai ta sa baki a lokuta da dama. Mun yi ta kiran gwamnan babban bankin na CBN karo na farko, amma ya ki amsa, saboda muna da tambayoyi masu wuya a gare shi.
“Har sai da na bayar da barazanar kama shi kafin ya zo, kuma da na sanya hannu kan wannan takardar; zai kasance karo na farko a tarihin majalisar dokokin kasar da aka kama wani gwamnan CBN. Da zan yi.
“Da yawa sun yi muhawara kan ‘yancin cin gashin kai na CBN, cin gashin kansa na CBN. Hakan bai sa CBN ya fi karfin doka ba. Kundin tsarin mulki ya baiwa majalisa ikon bayar da sammacin kama kowa, muna iya kiran kowa, kuma haka majalisar zata yi har sai gwamnan CBN ya zo.
“Don haka, muna kallo, kuma muna sa ido sosai. Idan akwai bukata, za mu sake kiran majalisa, duk da cewa duk mun tafi zaben mu. Zan sake kiran majalisar idan bukatar hakan ta taso”.
