Kasuwanci
Ganduje Ya Bada Umarnin Garkame Wani Shagon Siyar Da Kayayyaki A Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta hannun hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki, a ranar Lahadi, ta rufe babban kanti mai suna Wellcare, saboda kin karbar tsoffin takardun kudin Naira, Daily Trust ta rawaito.
A cewar mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi, an rufe babban kanti ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin.
Ya ce umarnin rufe kasuwar ya biyo bayan kin karbar tsoffin takardun kudin naira daga hannun kwastomominsu na WellCare Supermarket wanda ya sabawa umarnin gwamnatin jihar.
Gwamnatin Kano ta gargadi sauran ‘yan kasuwa a Kano da su sani cewa gwamnatin jihar ba ta hana amfani da tsofaffin takardun kudin Naira ba, don haka duk wani shago da aka kama bai karbi tsohon takardun kudin ba, za a yi hukunci mai tsauri akan sa.
Jim kadan bayan rufe kasuwar, Wellcare Alliance Limited ta rubuta wasikar neman gafara ga gwamnati, inda ta nemi a gaggauta shiga tsakani don sake bude babban kanti.
