Labarai
Yadda Wani Limamin Coci A Abuja Ya Fito Wa’azi Dauke Da Bindigar AK-47
Shugaban cocin House on the Rock, da ke Abuja, Fasto Uche Aigbe, a ranar Lahadin nan, ya hau kan mambarin wa’azinsa dauke da bindigar AK-47.
Wannan ya haifar da yanayi mamaki da cece kuce yayin da jama’a ke ƙoƙarin gano dalilin da ke tattare da irin hakan.
Faston ya ce “A yau, akwai wasu fastoci da baiwar duba da suke ta ƙwacewa mutane.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa ya kamata mu ɗauki ‘bindigu’ mu kare kanmu.
Zan zo musamman nan ba da jimawa ba ga wasunku da ke barci a cocin,” in ji shi yayin da mutanen cocin suka fashe da dariya.
