Connect with us

Labarai

Dalilin Da Yasa Aka Cire Naja’atu Muhammad Kwanaki Kadan Kafin Babban Zabe

 

Hukumar lura da aikin ‘yan sanda ta kasar nan ta maye gurbin Hajiya Naja’atu Mohammed, a matsayin ɗaya daga cikin masu sanya idanu na hukumar da za su lura da ayyukan ‘yan sanda a yankin arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an janyo hankalin hukumar ne kan wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja’atu na goyon bayan wata jam’iyya don haka APC take gani ba za ta yi wa jam’iyyar adalci ba.

A sanarwar da APC ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar Festus Keyamo ya yi watsi da naɗin Hajiya Naja’atu a matsayin mai lura da ayyukan ‘yan sanda a lokutan zaɓen ƙasar.

Sanarwar da hukumar ‘yan sandan ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton ‘yan sandan ƙasa Bawa Lawan domin lura da ayyukan ‘yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.

Hukumar ta ce a koda yaushe tana taka-tsan-tsan a ayyukanta kuma za ta ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da wanzuwa dimokradiyya a ƙasar.

Haka kuma ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da samun sahihin zaɓe a ƙasa nan.

Hukumar ta sanar da nadin Naja’atu da karin wasu mutane 44, domin sanya ido kan yadda jami’an yan sanda zasu gudanar da ayyukan su a yayin zaben 2023.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet