Hukumar jin daɗin Alhazai ta jihar Katsina ta umarci maniyyata aikin hajjin bana na jihar da su biya Naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar a matsayin kuɗin kafin alƙalami.
Shugaban hukumar Alhaji Suleiman Nuhu Kuki, ne ya bayyana hakan Yayin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Katsina.
Ya ce, hukumar kula da harkokin Alhazai ta ƙasa ta ware wa jihar ta Katsina kimanin kujeru 4,913 a aikin hajjin na bana.
Alhaji Suleiman Nuhu-Kuki Kuki ya kuma ƙara da cewa maniyatan za su biya kuɗin ne ta hannun hukumar, har zuwa lokacin da hukumar Alhazai ta ƙasa za ta sanar da ainihin kuɗin kujerar aikin hajjin na bana.
“Bayan da ƙasar Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000, hukumar aikin haji ta ƙasa ta ware wa jihar Katsina kujeru 4,913” a cewarsa.
Haka kuma ya ce, “Kuma gwamna ya bayar da umarnin raba kujerun ga ƙananan hukumomi 34 da ke faɗin jiharmu domin fara shirin aikin hajjin ga maniyatan jihar,” in ji Alhaji Nuhu-Kuki
BBC ta ruwaito cewa, shugaban ya ce, “Duk waɗanda ke da damar biyan kuɗinsu, su yi amfani da wannan dama wajen biyan kuɗaden ajiyarsu a kan lokaci, domin kuwa za a yi la’akari da wanda ya fara biyan kuɗi ne idan aka zo yin rajista”.
