A cewar Jami’ar ta ɗauki matakin korar daliban ne bayan zaman da majalisar malaman jami’ar ta gudanar a ranar 26 ga watan jiya na Janairu.
Haka kuma ta ce akwai wasu ɗaliban na daban da za su sake maimita shekara ɗaya.
Jami’ar ta Bayero, ta kuma ja kunnen wasu ɗaliban fiye da su ashirin kamar yadda Jami’inta na hulɗa da jama’a Lamara Garba, ya bayyana.
