Labarai
An Kama Wani Dan Majalisa Dauke Da Makudan Kudin Kasar Waje
An kama wani dan majalisar wakilai, Dokta Chinyere Igwe da wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba, Punch ta rawaito.
Igwe, wanda ke wakiltar mazabar tarayya ta Fatakwal 2, a majalisar wakilai ta kasa, an kama shi ne da safiyar ranar Juma’a a kan titin Aba a Fatakwal.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, wadda ta tabbatar wa da wakilinmu kamen, ta ce nan ba da jimawa ba za a fitar da wata sanarwa a kai.
An ce Igwe yana goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne.
