Featured
Hukumar Shari’a Ta Bukaci A Gudanar Da Zabe Cikin Kwanciyar Hankali
Hukumar Shari’ar Musulunci ta jihar Katsina ta bukaci mazauna yankin da su gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali domin zaben ‘yan takarar da suke so ba tare da tashin hankali ko tsangwama ba.
Shugaban hukumar, wanda kuma shi ne Grand Khadi na jihar, Dr Muhammad Abubakar, ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Katsina a wani taron manema labarai.
Abubakar ya ce a mahangar addinin Musulunci, zabuka da tsarin zabe na nufin a ba ‘yan kasa dama da ba su damar gudanar da ayyukansu na jama’a wajen zaben shugabanni da wakilan da suke so.
Ya ce saboda haka su daure su tabbatar sun yi amfani da irin wadannan hakkoki da zabi cikin lumana.
Shugaban ya yi ishara da fadin Allah a cikin Alkur’ani, sura ta 2, aya ta 195: “…. Kuma kada ku jefa kanku da hannuwanku zuwa ga halaka. Kuma ku kyautata; Lallai Allah Yana son masu kyautatawa”.
Ya ci gaba da cewa, Musulunci gaba daya ya yi hannun riga da tashin hankali, zalunci, mugubta, ’yan daba da duk wani aiki da ake da nufin tsoratarwa, muzgunawa ko haddasa fitina ga jama’a.
Abubakar ya kara da cewa, Annabi Muhammad (SAW) ya ce: “Ya ishi musulmi zunubi ya wulakanta dan uwansa musulmi.
“Dukkanin al’amura na zalunci musulmi haramun ne ga dan’uwansa musulmi: jininsa da dukiyarsa da mutuncinsa”.
Ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan siyasa da masu kada kuri’a suna bin Dokokin zabe da tsari da ka’idojin zabe da kuma dokar hana kalubalan tsaro da gwamna ya sanya wa hannu.
