Featured
Kotu Ta Ayyana Zaben Gwamnan Zamfara A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta soke nasarar da Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ya samu.
A cewar kotun, hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen Gwamnan ta yi a baya, wanda ya tabbatar da nasarar Dauda, bai yi la’akari da hujjar da jam’iyyar APC mai ƙara ta gabatar ba.
A don haka kotun ta bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.
