Featured
Makonni biyu bayan sace limaman da suke je addu’ar neman nasarar Tinubu, har yanzu ba a san inda suke ba
Makonni biyu bayan da ‘yan bindiga suka sace limaman Juma’a biyar a Jihar Zamfara, har yanzu ba a san inda suke ba. An sace su ne a ranar 13 ga Satumba yayin da suke tafiya Talata Mafara domin halartar addu’ar samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
‘Yan bindigar sun yi garkuwa da limaman ne a Gidan Suleiman Bature, kimanin kilomita uku daga ƙauyen Damri. Rundunar ‘yan sandan Zamfara ta ce ta fara wani samame domin ceto limaman, yayin da iyalansu da al’ummominsu ke cikin damuwa kan halin da suke ciki.
Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin limaman ya ce ‘yan bindigar sun rage kuɗin fansa daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 30 bayan tattaunawa da wakilan al’ummomin da abin ya shafa.

Pingback: Atiku ga Tinubu: Ka yi bayanin yadda aka kashe tsoffin basussuka, kafin ciyo sabon bashin dala biliyan 1.5 - KAKAKI 24