Featured
Gwamnatin Tinubu ta amince da ba wa ma’aikata tallafin 70,000 duk wata na tsawon watanni shida
Gwamnatin Najeriya ta amince da biyan ma’aikata alawus na sufuri na Naira 70,000 duk wata, na tsawon watanni shida, daga watan Nuwamba 2026, domin rage raɗaɗin matsalolin tattalin arziki.
An cimma matsayar ne a ƙarshen wani taron sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da aka gudanar a ranar Talata a Abuja, kan walwala da jin daɗin ma’aikata.
Read Also : Mun samu masu son saka hannu jari a matatar mu daga kasashe 120 na duniya – Dangote
Tawagar gwamnati ƙarƙashin Ministan Kwadago, Dokta Muhammad Dingyadi, da Darakta Janar na Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, tare da shugaban NLC, Joe Ajaero, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar. Tallafin zai shafi ma’aikata a dukkan matakan gwamnati.
Haka kuma, an amince za a biya ma’aikatan lafiya alawus-alawus na watanni 19 cikin watanni uku daga Disamba 2026. Ɓangarorin sun kuma amince da kafa kwamiti kan mafi ƙarancin albashi, tare da sake ganawa bayan wata guda domin tantance aiwatar da yarjejeniyar.
