Featured
Atiku ga Tinubu: Ka yi bayanin yadda aka kashe tsoffin basussuka, kafin ciyo sabon bashin dala biliyan 1.5
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ci gaba da ciyo sabbin basussuka, yayin da ‘yan Najeriya ke cigaba da fuskantar tsadar abinci, man fetur da wutar lantarki.
Atiku ya mayar da martani ne kan shirin gwamnatin tarayya na karɓar sabon bashin dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya, yana mai cewa, ya kamata gwamnati ta fara yin bayani kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen basussukan da aka karɓa a baya, kafin a ciyo sabon bashi.
Read Also : Makonni biyu bayan sace limaman da suke je addu’ar neman nasarar Tinubu, har yanzu ba a san inda suke ba
Ya ce ya kamata gwamnati ta bayyana ayyukan da za a gudanar da sabon bashin, al’ummomin da za su amfana, manufofin da aka sanya, sharuddan bashin da kuma lokacin aiwatar da ayyukan. Atiku ya kuma tambayi dalilin da ya sa bashin ƙasar ke ci gaba da ƙaruwa duk da ikirarin gwamnati na samun ƙarin kuɗaɗen shiga.

Pingback: Talauci zai ƙara ta’azzara a Arewacin Najeriya matuƙar Tinubu ya faɗi zaɓe a 2027 - APC - KAKAKI 24