Featured
Kaduna: Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta bayyana zaɓen gwamna a matsayin wanda bai kammala ba
Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe da ke zamanta a Kaduna ta kori Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC
Dan takarar jam’iyyar PDP, Isah Mohammed Ashiru ne ya shigar da karar bisa rashin gamsuwa da zaben da aka yi.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Kotun, a ranar Alhamis din nan, ta bayyana zaɓen gwamna na 2023 a jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
Tun da farko a korafin Uba Sani ya nemi kotu ta kori ƙarar da ɗan takarar jam’iyyar PDP ya shigar, inda yake kalubalantar nasarar dan takarar APC.
Lauyoyin Gwamna Uba Sani sun bayar da hujjar cewa an shigar da karar ne bayan karewar wa’adin kwanaki 21 na shigar da kara, idan mutum bai gamsu da zaben ranar 18 ga watan Maris na 2023 ba.
A martanin da ya bayar, kwamitin alkalai mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Victor Oviawe ya tabbatar da cewa an shigar da ƙarar ne a ranar 10 ga watan Afrilu, inda kotu ta yi watsi da hujjar Uba Sani wanda ake kara na biyu.
