Featured
EFCC Ta Gurfanar Da Wata ‘Yar Kasuwa A Gaban Kuliya Bisa Zargin Damfarar N4.4bn
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Najeriya EFCC, a ranar Alhamis, ta gurfanar da wata ‘yar kasuwa mai suna Florence Onojame a gaban kuliya bisa zargin damfarar N4.4bn.
Onojame, tare da kamfaninta, Emee Oil & Gas Nigeria Limited, an gurfanar da su a gaban mai shari’a Mojisola Dada na kotun manyan laifuka ta Legas da ke Ikeja.
Laifukan da ake tuhumarta guda uku da aka shigar mata da kamfaninta sun shafi hada baki da zamba.
Lauyan hukumar EFCC mai shigar da kara, Fatai Mohammed, ya shaida wa kotun cewa ‘yar kasuwar man ta hada baki da wasu mutane wajen damfarar Access Bank Plc kudi Naira 4,380,100,000.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta yi zargin cewa ta karkatar da kudin ta hanyar Primusplus, wani dandali na bankin Access na lantarki, sannan ta kara tura kudaden zuwa wasu asusun ajiyar banki.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa ta aikata laifin ne a watan Fabrairun 2022 tare da hadin gwiwar wani da ake tuhuma, Chris Nnaji, Captain Robert Aboh, Emenike Vincent Ebulu da kuma Nuhu Amanabo wadanda yanzu haka suke hannun hukumar.
A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da sashi na 409, 278, da 285 na dokar laifuka ta jihar Legas, na shekarar 2011.
Sai dai wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifukan uku da ake tuhumar ta da su.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa A bisa bukatar masu gabatar da kara, Mai shari’a Dada ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Onojame a gidan yari na Ikoyi, yayin da ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba domin duba bukatar bayar da beli.
