Featured
Zan iya sadaukar da rayuwata wajen ganin Tinubu ya yi nasara a 2027 – Uba Sani
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada aniyarsa ta kare takarar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2027, yana mai cewa zai iya sadaukar da rayuwarsa domin ganin shugaban ya yi nasara.
Gwamnan ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu ya samo asali ne daga gamsuwarsa da salon mulkin shugaban ƙasar da kuma yadda yake gudanar da al’amuran ƙasa.
Read Also : Reassessment of DSP Barau’s Projects in Kano North: One Building, Three Names (1)
Uba Sani ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da suka sa yake goyon bayan Tinubu shi ne dangantakar da ta daɗe a tsakaninsu, wadda ta samo asali tun shekarar 1994.
A cewar gwamnan, dangantakar tasu ta samo asali ne a lokacin da suke fafutukar dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Pingback: Mun samu masu son saka hannu jari a Matatar mu daga kasashe 120 na duniya - Dangote - KAKAKI 24