Featured
Muna iya kokarinmu wajen ganin an ceto Ahmad Zakka da iyalainsa – Gwamnatin Kaduna
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce tana matukar ƙoƙarin wajen ganin an ceto wani magidanci da matarsa da jaririyarsu, waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a unguwar Millennium City.
Bidiyon iyalan da aka sace, wanda ya nuna su cikin mawuyacin hali a hannun masu garkuwa da mutanen, ya jawo kakkausar suka daga ’yan Najeriya, ciki har da jagoran ’yan adawa, Atiku Abubakar, wanda ya yi kira da a gaggauta ceto su.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki, ya ce bisa umurnin gwamnan jihar, suna ci gaba da tattaunawa da jami’an tsaro domin ceto iyalan da kuma ƙara tabbatar da tsaron rayukan al’ummar yankin.
Ya ce gwamnati tana sane da lamarin tun kafin ɓullar bidiyon, kuma tun daga wannan lokaci ta fara ɗaukar matakan da suka dace. A baya, rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wasu da ake zargin suna da alaƙa da garkuwa da iyalin.

Pingback: Gwamnatin Tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhuma kan mutumin da ake zargi da kirkirar hukumar bogi - KAKAKI 24