Featured
Bauchi: Ƴan sanda sun kama wani ɗan jarida bisa umarnin gwamna
Jami’an rundunar ƴan Sanda sun kama Haruna Salisu Mohammed, shugaban kafar yaɗa labarai ta WikkiTimes dake Bauchi lokacin da yake tsaka da gudanar da aiki tare da tsare shi a sashin binciken masu laifuka (CID) dake babbar shalkwatarsu.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa an kama Harunan ne daidai lokacin da yake gudanar da aikinsa na jarida a zaɓen da ake yi ranar Asabar a garin Duguri wanda shi ne tushen gwamna Bala Mohammed.
Kafin masu fushi da fushin wani su kama ɗan jaridar dai, Haruna yana yin hira ne da wasu mata da suke nuna rashin jin daɗinsu dangane da yadda akai musu alƙawarin ɗaukar aiki ta hanyar karɓar takardunsu (CV) Amma kuma aka share su.
Suna tsaka da hirar ne sai matan suka ce su sun ma fasa yin zaɓen.
kwatsam sai wasu ƴan daba suka durfafo wurin, waɗanda ake zaton magoya bayan gwamnan Bauchi ne suka yi ƙoƙarin yiwa Haruna rotse.
Kafin faruwar hakan ne jami’an ƴan sanda suka tsere da shi ofishinsu.
Da farko jami’an sun ce sun tafi da shi ne saboda tserar da shi daga ƴan daban amma kuma sai suka ƙi sakinsa wai har sai gwamna Bala Mohammed ya ba su umarni.
Kawo yanzu Haruna Muhammad ya shafe sama da awanni 24 a tsare ba tare da wata tuhuma ko sakinsa ko kuma bayar da belinsa ba. Kuma ba zasu sake shi ba sai sun sami umarni daga gwamnan Bauchi. A cewar editan jaridar WikkiTimes Yakubu Mohammed.
Sai wata tuhuma da aka ce wai ƴan sandan sun ce “ana tuhumarsa da aikawa da bidiyon zanga-zangar nuna rashin jin daɗin da matan suke yi zuwa ga jam’iyyar adawar gwamnan ta APC”
Sai dai kuma “Ni ma tura min video aka yi kuma har ƴan sandan ma sun caje waya ta bayan ɗaukar bayanai na” a cewar Haruna.
Jami’an ƴan sandan har kawo yanzu sun gaza bayar da jawabi mai ma’ana dangane da lamarin ɗan jaridar ga manema labarai, bayan sun kama shi tare da tsare shi.
Wanda hakan yake a matsayin take masa haƙƙin gudanar da aiki da kuma ƴancinsa na ɗan ƙasa da kuma na ɗan Adam.
