Connect with us

Labarai

Zargin kashe Ƴan Kwankwasiyya: Jami’an tsaro sun cafke Alasan Ado Doguwa

 

Jami’an ƴan sanda sun cafke shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai Alasan Ado Doguwa bisa zargin sa da hannu wajen tada rikicin da ya yi sanadiyyar kashe mambobin jam’iyyar NNPP.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, ƴan sanda sun cafke Alasan Ado ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da yammacin yau Talata yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgi zuwa Abuja.

Haka kuma ta ruwaito cewa ana zargin ɗan majalisar ne da jagorantar kai hari ofishin jam’iyyar NNPP a garin Tudunwada tare da cinna wuta a ofishin inda mutane 2 suka mutu sakamakon ƙonewa da suka yi.

Wasu mutanen kuma sun jikkata suna kwance a asibiti.

Jaridar ta kuma ce, tuni jami’an suka miƙa shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan jihar Kano.

Sai dai duk ƙoƙarinta na jin ta bakin mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa hakan bai samu ba kasancewar ba ta same shi a waya ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet