Connect with us

Labarai

Alhassan Ado Doguwa Ya Kuma Darewa Kujerar Wakiltar T/Wada, Doguwa

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta bayyana Honarabul Alhassan Ado Doguwa na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa.

Jami’in hukumar zabe INEC daga jami’ar Bayero da ke Kano Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai na sashin kimiyyar hada magunguna ne ya bayyana sakamakon.

Farfesa Yakasai ya ce an gudanar da zabe lafiya kuma an gama lafiya, hasali ma ga sakamakon zaben da kowace jam’iyya ta samu.

Bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka kawo: Abdurrhman Mustapha Hamza na jam’iyyar ADC ya samu kuri’u 152, Alhasan Ado Doguwa ya samu kuri’u 39,732, Yusha’u Salisu Abdullah na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 32,798.

Haka kuma Jamilu Zaben Dayyabu na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 2,091, Sai Auwal Salisu na jam’iyyar PRP ya samu kuri’u 105.

Wanda haka ya nuna cewa Alhasan Ado Doguwa ya samu nasarar lashe wannan zabe bisa yadda ya samu kuri’u mafi rinjaye Kamar yadda doka ta tanada.

Alhassan Ado Doguwa Sardaunan Rano (OON) wanda dama shi ne dan majalisar da ke wakilatar kananan hukumomin Tudun Wada da Doguwa a zauren majalisar kuma shugaban masu rinjaye na majalisar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet