Connect with us

Featured

Ƴan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Sace Dagaci a Kano

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da hannu a garkuwa da Dagacin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 04 ga Oktoba, inda ya ce jami’an rundunar yaki da garkuwa da mutane sun cafke wanda ake zargin, Usman Lawan Baba mai shekara 27, wanda aka fi sani da “Yellow,” a ranar 2 ga Oktoba, 2025 a Dakatsalle, ƙaramar hukumar Bebeji.

An bayyana cewa Baba na cikin jerin waɗanda ake nema bisa laifin garkuwa da dagacin a ranar 9 ga Agusta, 2023, inda aka sace shi tare da kwace masa kuɗi Naira Miliyan 2.75, wayar Tecno Kevo 4, da agogo. Rundunar ’yan sanda ta yi nasarar ceto dagacin bayan ta tarwatsa ƙungiyar masu garkuwa da shi yayin ƙoƙarinsu na guduwa.

A yayin bincike, Baba ya amsa laifinsa inda ya bayyana cewa ya samu ₦6,000 daga cikin ganimar, kuma ya bayyana sunayen wasu abokan aikinsa. Daga cikin su akwai Bello Kici-Kici daga Doguwa wanda aka kashe yayin wani samame; Mallam Sale daga Gezawa wanda aka kashe a yayin fashi; da kuma Ruwa Shehu daga Bebeji wanda ke zaman hukunci a gidan gyaran hali. Sauran mutum uku, ciki har da Ibrahim Gwanja da Sule Naye, har yanzu ana ci gaba da bincike a kansu.

Rundunar ta tabbatar cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike. Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewar sashen yaki da garkuwa da mutane da kuma gudunmawar al’umma wajen taimakawa jami’an tsaro. Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaki da masu aikata laifuka domin tabbatar da tsaro a jihar.

Share this:
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetDeneme Bonusu Veren SitelerCasibomcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahisjojobetjojobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobetjojobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet