Featured
Jami’ar ABU Na Kashe Naira Biliyan 4 a Kowacce Shekara Kan Wutar Lantarki – VC
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta bayyana cewa tana kashe kusan Naira biliyan 4 a kowace shekara wajen biyan kudin wutar lantarki, lamarin da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Ahmed, ya bayyana a matsayin mai “tsanani da kuma barazana ga ayyukan jami’ar.” Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai na murnar cikar jami’ar shekara 63 da kafuwa, inda ya ce tsadar wuta na shafar gudanar da bincike da koyarwa, tare da dagula tsarin aiki.
Farfesa Ahmed ya ce dogaro da wutar gwamnati abu ne mai wahala a yanzu, saboda rashin tabbas da tsada, don haka jami’ar ta fara ɗaukar matakan samar da hanyoyin makamashi masu ɗorewa domin rage kashe-kashe da inganta samar da wuta. Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 1 ta hannun TETFund don magance matsalar, tare da amincewa da wani shiri da zai samar da megawatt 10 na makamashin sabuntawa.
Ya ƙara da cewa jami’ar ta kuma nemi goyon bayan tsoffin ɗalibai, musamman ajin SBS na 1975, waɗanda ke aiwatar da aikin hasken rana domin ɗaya daga cikin cibiyoyin CBT. A cewarsa, ABU tana ɗaukar alhakin makomarta ne ta hanyar ƙirƙira da haɗin gwiwa da abokan ci gaba domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Farfesa Ahmed ya kuma yi amfani da bikin zagayowar jami’ar wajen tunawa da hangen nesa na marigayi Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello, wanda ya kafa jami’ar a 1962 domin horar da ƙwararru da haɗa kan Najeriya. Ya ce duk da kalubalen tsaro da talauci da ke addabar Arewa, ABU za ta mayar da hankali wajen gudanar da bincike da shirye-shirye na magance waɗannan matsaloli.
