Labarai
Zargi: Jam’iyyun PDP, LP, Da ADC Sun Bukaci Shugaban INEC Ya Gaggauta Yin Murabus
Jam’iyyun LP, PDP, da ADC, sunyi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da ake ci gaba da tattara wa Yanzu haka a shalkwatar tattara sakamakon dake Abuja.
Shugaban Jamiyyar LP yace sakamakon da hukumar ke bayyanawa ya saba da ainihin sakamakon da suka samu daga fadin kasar nan.
Yace hukumar ta gaza dora sakamakon a shafin yanar gizo kamar yadda tayi alkawari.
Naurar BVAS Bata yi Aki ba a wurare da dama, wanda hakan ya bayar da damar aringizon kuri’a.
Yace babu adalci a cikin wannan zabe, Kuma shugaban hukumar zabe Mahmud yakubu ya basu kunya.
Sun Kuma dawo daga rakiyar shugaban hukumar ta INEC, inda suka bukaci da ya sauka daga mukaminsa cikin gaggawa ya kyale wani daban ya kammala wannan aiki.
Sun yi Kira ga shugaban kasa da ya cika alkawari sa na ganin ya tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe.
Daga karshe an sanya sautin muryar farfesa Mahmud Yakubu shugaban hukumar zaben, inda yake karyata batun cewa hukumar ba zata dora sakamakon zaben a shafin yanar gizo ba.
