Labarai
Jihohi 6 sun buƙaci kotun ƙoli ta rushe zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisa
Jihohi shida na Nijeriya, sun buƙaci kotun ƙoli ƙasar da ta soke zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga Faburairu.
Jihohin sun buƙaci hakan ne ta cikin wata ƙara da suka shigar a kotun ƙolin
BBC ta ruwaito cewa, jihohin sun haɗa da Adamawa da Akwa Ibom da Bayelsa da Delta da Edo da kuma Sokoto.
Haka kuma ta ƙara da cewa, sun buƙaci kotun da ta yi amfani da tanade-tanaden doka wajen soke zaɓen la’akari da irin kura-kurai da kuma zargin an tafka maguɗi yayin zaɓen.
