Labarai
Mun gyara kura-kuran da muka samu a baya domin tunkarar zaɓen gwamnoni- INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC, ta bayyana cewa ta gyara matsalolin da ta fuskanta lokacin zaɓen Shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya tare da shirya wa tsaf wajen tunkarar zaɓen gwamnoni.
Kwamishinan wayar da kan masu zaɓe na hukumar Mista Festus Okoye, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.
Mista Pestus Okoye, ya ce, hukumar ɗauki manyan darusa a zaɓen na baya kuma za ta yi llkuma za ta gyara kura-kuran a zaɓen gwamnoni da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
Haka kuma, ya ƙara da cewa, Hukumar ta INEC na yin iyakar kokari domin magance matsalar a sashen duba sakamakon zabe na shafin hukumar domin riƙa ɗora shi tun daga rumfunan zaɓe.
