Labarai
Adadin Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Tashi Zuwa 21.91% — Hukumar NBS
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce hauhawar farashin kayayyaki a kasar ya karu zuwa kashi 21.91 a watan Fabrairun 2023 idan aka kwatanta da kashi 21.82 na watan Janairun 2023, wanda ya nuna karuwa da kashi 0.09 cikin dari.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta mai suna ‘Kididdigar Farashin Mabukaci a (Fabrairun 2023)’ kamar yadda Gidan Talabijin na Channels ya rawauti a ranar Larabar nan.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfadowa daga karancin kudin Naira na watanni da suka biyo bayan shirin sake fasalin Naira na Babban BankinKasa (CBN) da aka fara a ranar 26 ga watan Oktoban 2022.
A watan Nuwambar 2022 ne dai CBN ya kaddamar da sabbin takardun kudi na Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1,000 a wani yunkuri na magance matsalar tara kudade da siyan kuri’u gabanin babban zabe na 2023.
An aiwatar da tsawaita wa’adin a ranar 10 ga watan Fabrairu a daidai lokacin da kotun koli ta yanke hukuncin da ya ba da izinin amfani da tsoffin kudaden.
“A cikin watan Fabrairun 2023, hauhawar kayayyaki ya tashi zuwa 21.91% idan aka kwatanta da watan Janairu 2023 farashin wanda ya kasance 21.82%,” in ji shi.
“Duba abin da ke faruwa, hauhawar farashin kayayyaki a watan Fabrairun 2023 ya nuna karuwar maki 0.09% idan aka kwatanta da farashin na watamJanairu 2023.”
Hakazalika, a duk shekara, farashin ya kai kashi 6.21 bisa dari, idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Fabrairun 2022, wanda ya kai kashi 15.70 cikin dari.
