Featured
Babu wata jam’iyya ko dan takara da muke goyon baya – INEC
Kwamishinan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Maj-Gen. Modibo Alkali ya ce hukumar ba ta da wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara da ta ke mara wa baya a kasar.
Alkali ya bayyana haka ne a taron masu ruwa da tsaki da aka yi da wakilan dukkanin jam’iyyun siyasa a Talatar nan a jihar Sakkwato.
Ya ce hukumar zaben ba za ta lamunci maimaita kura-kurai da aka samu a zaben shugaban kasa da na ƴan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata ba.
