Labarai
Zaɓe: Sarki Amin Ado Bayero ya umarci Hakimi da Dagatai su sanya ido kan baƙin fuska
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bai wa masu unguwanni da Hakimai da kuma Dagatai umarnin sanya ido wajen shige da ficen baƙin fuska a yankunan su lokacin zaɓe.
Sarkin ya bayar da umarnin ne yau Juma’a, yayin da yake yin jawabi ga manema labarai a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ƙara da jan hankali da mutane kan su fita su yi zaɓen gwamnoni da ƴan majalisun jiha a gobe Asabar kamar yadda yake bisa tsarin dokar ƙasa.
Haka kuma, Sarkin ya ja kunnen ƴan siyasa da su ƙaurace wa mummunar ta’adar nan ta sayen ƙuri’ar mutane da kuma haifar da abinda zai janyo zubar da jini.
