Labarai
Da ɗumi-dumi: Gwamnatin Kano ta sanya dokar hana fita
Gwamnatin jihar Kano, ta sanya dokar hana fita daga safiyar yau Litinin zuwa dare.
Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai Malam Muhammad Garba, ya fitar da safiyar yau.
Sanarwar ta ruwaito cewa, an sanya dokar ne domin daƙile duk wani yunƙurin tayar da tarzoma bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamna.
Wannan dai na zuwa ne mintoci kaɗan bayan da hukumar INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar gwamnan Kano.
