A karo na biyu, Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya sake samun nasarar lashe zaɓe zuwa wa’adi na biyu na mulkin jihar.

Hakan dai ya biyo bayan nasarar gwamnan ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar ransar Asabar ɗin da ta gabata.

Hukumar INEC ta bayyana Babagana Umarah Zulum a matsayin wanda ya lashe zaɓen a yau Litinin.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Gwamna Zulum ya lashe zaɓen ne da ƙuri’a 545,542 sai kuma jam’iyyar PDP ta ke da ƙuri’u 82,147.

Ita kuwa Jam’iyyar LP ta zo ta uku da kuri’a 1,517.