Labarai
‘Yan Najeriya Mazauna Amurka Na Wani Shiri Na Kawo Karshen Rashin Zuwan Yara Makaranta
‘Yan Najeriya mazauna Birtaniya sun tara kimanin Naira miliyan 23 a yunkurinsu na fara magance matsalar rashin zuwa makaranta a Najeriya da ya tilastawa yara miliyan 20.2 barin makaranta.
An tara kudaden ne a wani bikin taya juna murna wanda kungiyar agaji ta kasa da kasa, IA-Foundation ta shirya a Landan ranar Laraba.
A cikin sakon imel da ta aike wa Kamfanin dillancin Labarai na Kasa (NAN) game da taron, babbar jami’ar IA-Foundation, Misis Ibironke Adeagbo, ta ce ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban na kasar Birtaniya sun halarci taron.
Ta ce ‘yan Najeriya sun halarci taron da dama, duka dai domin nuna goyon bayansu ga kokarin da IA-Foundation ke yi na magance matsalar rashin zuwa makaranta a kasar da ke yammacin Afirka.
Najeriya, wacce ke kan gaba wajen fitar da man fetur a Afirka, tana da dimbin al’umma a halin yanzu ba sa zuwa makaranta, a cewar hukumar raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO.
Sai dai kuma kungiyar IA-Foundation mai rijistar Burtaniya ta tashi tsaye wajen fuskantar kalubale tun daga shekarar 2019 a kokarinta na shawo kan matsalar tare da ganin kasashen duniya da gwamnatin Najeriya su tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen.
A jawabin da ta gabatar a wurin taron hada kudi , Adeagbo ta jaddada bukatar mutane masu kishin kasa su taimaki Najeriya wajen ceto makomar ‘ya’yanta.
Ta ce akwai bukatar ‘yan Najeriya a duk inda suke a duniya su yi hadin gwiwa a fannin zamantakewar al’umma a fannin ilimi don sanya kowane yaro dan Najeriya a makaranta.
Adeagbo ya yi nuni da cewa, bai kamata a yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an baiwa yara miliyan 20.2 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya damar samun ilimi mai inganci.
