Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Mista Godwin Emiefele, ya nemi afuwar ƴan Najeriya bisa matsalolin da ake fuskanta yayin tura kuɗi ta Internet.
Mista Godwin Emefiele, ya buƙaci hakan ne yayin taron kwamitin tsare-tsare kan harkokin kuɗi da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Haka kuma, ya tabbatar da cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba kamar yadda shafin BBC ya ruwaito.
Gwamnan na babban banki, ya ƙara da cewa, sashen da ke kula da biyan kuɗaɗe na babban bankin, na yin iyakacin kokarinsa wajen tabbatar da cewa an magance matsalar.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli wajen aika kuɗi da wayoyinsu na hannu har ma a na’urar hada-hadar kuɗi ta POS.
