Labarai
Gwamna Matawalle ya karɓi ƙaddarar shan kaye daga Dauda Lawal Dare
Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya rungumi ƙaddarar shan kaye a zaɓen da ya sha kaye a hannun Dauda Lawal Dare na jam’iyyar PDP.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta cikin wani saƙon murya da ya fitar ga al’ummar jihar.
Ta cikin saƙon, gwamna Matawalle ya ce, sun karɓi ƙaddamar shi da magoya bayansa na jam’iyyar APC mai mulkin jihar.
Haka kuma ya ƙara da neman afuwar duk wanda ya ɓata wa a matsayinsa na gwamnan jihar mai barin gado.
