Connect with us

Labarai

Kotu Ta Bada Umarnin Tsare Mutane Uku Bisa Zargin Mallakar Takardun Dangwalen Kuri’a

 

Babbar Kotun Majistare ta Minna mai lamba 3, dake da matsiguni a Babbar Kotun Koli ta bayar da umarnin tsare wasu mutane uku a gidan gyaran hali bisa samunsu da laifin mallakar takardar dongwala kuri’a, fom din sakamakon zabe da kuma sace na’urar BVAS.

Jami’an ‘yan sanda na yankin Agaie ne suka kama mutane ukun da ake zargin suna da kayan zabe da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a garin Agaie.

Wadanda ake tuhuma; Usman Aliyu, Mohammed Mohammed da Salihu Mohammed, an gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhume-tuhume hudu da suka hada da hada baki, mallakar takardar dongwala kuri’a, kwace na’urar BVAS mai lamba 26.01.10001 da sauran kayan zabe da kuma rashin baiwa ma’aikacin gwamnati bayanai.

A cewar rahoton farko na ‘yan sanda (FIR), na Insifekta Emmanuel Bassa,yace tuhume-tuhume hudun da ake tuhumar su da su za’a iya hukunta su ne a karkashin sashe na 97 na kundin penal code da sashe na 115(2)126(1) na dokar zabe, 2023.

Rahoton ‘yan sanda mai lamba MN/CR/20/2023 ya bayyana cewa, a ranar 18 ga watan Maris, 2023, yayin tattara sakamakon zaben gwamna da na ‘yan majalisar jiha a Bugama, mazabar Magaji ta Agaie, wasu ‘yan daba sun mamaye sashen zaben. kuma sun nuna rashin adalci, sun yiwa jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) barazana, sun kwace na’urar BVAS mai lamba 26.01.10001 da sauran kayan zabe.

“’Yan sanda sun zage damtse a inda abin ya faru suka kwato kayan INEC sannan suka kama ku, Usman Aliyu, Mohammed Mohammed, Salihu Mohammed, duk a yankin Ekowuma dake kauyen Buhama ta Agaie.

“Binciken da ‘yan sanda suka yi ya nuna cewa kai Mohamed Mohammed,da kai Salihu Mohammed, duk kun san matsayin kayan hukumar INEC kuma kun gaza, kuka yi sakaci da kuma kin ba wa ‘yan sanda bayanai da gangan, don haka ake zargin ku da aikata laifukan da ke sama.”

A lokacin da Alkalin Kotun Mai shari’a Ahmed Aliyu Musa ya karanta wa wadanda ake kara tuhume-tuhumen, dukkansu sun musanta aikata laifin, sannan mai gabatar da kara na ‘yan sandan, Insifekta Emmanuel Bassa ya bukaci da a dage shari’ar don baiwa ‘yan sanda damar kammala bincike tare da cafke wadanda ke kan lamarin biyo bayan batan dabon da suka yi.

Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Afrilu domin ci gaba da gabatar da shari’ar sannan kuma aka bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet