Connect with us

Labarai

Hukumar DSS Ta Kama Wani Dan Majalisar Dokokin Jiha Na Jam’iyyar PDP

 

Jami’an hukumar tsaron DSS sun kama wani zababben dan majalisar dokokin jihar Ogun, Damilare Bello.

Bello, wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP ne, ana zargin shi ne ya kitsa rikicin Sagamu da ya yi sanadiyyar lalata bankuna da dama a yayin zanga-zangar karancin naira.

Jaridar PUNCH ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun amsa gayyata da dama daga hukumar ta DSS.

Bello, wanda aka fi sani da Dre, an ce tun lokacin da lamarin ya faru, ya yi batan dabo amma ya fito a zaben na ranar Asabar da aka gudanar.

Wata majiya a hukumar DSS ta tabbatar wa da wakilinmu kamun Bello a ranar Laraba.

Majiyar ta ce, “An fara bincike na farko kuma ana iya gurfanar da wanda ake zargin da aikata laifukan da suka shafi kone-kone da hargitsa zaman lafiyar jama’a, da dai sauransu bayan kammala bincike.

“Kamen ba shi da nasaba da siyasa kamar yadda aka ruwaito.”

Sai dai kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Oladipupo Adebutu, ya kai ziyara ofishin DSS.

Majiyar ta shaida wa wakilinmu cewa, jam’iyyar PDP ta aike da tawaga daban-daban guda uku, karkashin jagorancin shugabanta, Sikirulah Ogundele, da wasu jiga-jigan kasar kan lamarin.

Majiyar ta ci gaba da cewa, “Adebutu da kansa ya ziyarci rundunar ne a ranar Laraba, da nufin dinke baraka da hukumar tare da kawar da munanan ra’ayoyin da aka yi a baya game da ofishin, ya kuma gane cewa ma’aikatar wata cibiya ce mai inganci da dole ne a yi la’akari da ita. ”

Mai taimaka wa Adebutu kan harkokin yada labarai, Afolabi Orekoya, ya tabbatar wa wakilinmu cewa shugaban nasa yana ofishin DSS.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisjojobetgrandpashabetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet girişjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet