Connect with us

Labarai

CBN Ya Umarci Bankuna Su Yi Aiki A Ranekun Karshen Mako, Ya Tabbatar Da Fitar Da Kudade

 

Babban bankin Kasa (CBN) ya tabbatar da kwashe takardun tsofaffin kudi daga rumbun ajiyarsa zuwa bankunan kasuwanci a fadin kasar, a wani mataki na hadin gwiwa na ganin an sassauta yaduwar takardun kudin a bankuna daban-daban.

Babban bankin na CBN ya kuma umarci dukkan bankunan kasuwanci da su bude aiki a ranakun Asabar da Lahadi.

Mukaddashin Daraktan Sashen Sadarwa na Babban Bankin na CBN, Dakta Isa AbdulMumin ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’ar nan, inda ya bayyana cewa, an samu makudan kudade a bangarori daban-daban da bankunan kasuwanci suka karba domin mikawa abokan huldarsu.

A cewarsa, babban bankin na CBN ya umurci dukkan bankunan da su zuba kudin a ATM dinsu tare da gudanar da ayyuka na zahiri a dakunan banki a karshen mako.

“Bankunan kasuwanci za su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi don biyan bukatun abokan ciniki,” in ji shi, ya kara da cewa Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, da kansa zai jagoranci tawaga don sanya ido kan matakin bin ka’ida ta hanyar bankunan a wurare daban-daban a fadin kasar.

Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri domin halin da ake ciki zai samu sauki nan ba da dadewa ba tare da yin rigakafin wasu takardun kudi a wurare daban-daban.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta umurci mambobinta da su mamaye ofisoshin babban bankin Kasa CBN a fadin kasar sakamakon karancin kudi.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet