Kasuwanci
NBS Ta Bayyana Yadda Farashin Kayan Abinci Yake Cigaba Da Hauhawa
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa farashin kayan abinci kamar su doya, shinkafa da naman sanya an samu karuwar farashin a cikin watan Fabrairu.
Wannan yana kunshe ne a cikin Rahoton Kallon Farashin Abinci na NBS na watan Fabrairu 2023 wanda aka fitar a Abuja ranar Juma’a.
Rahoton ya ce matsakaicin farashin naman shanu mai nauyin kilo 1 a kowace shekara, ya karu da kashi 27.43 bisa dari daga N1,922.2 a watan Fabrairun 2022 zuwa N2,445.96 a watan Fabrairun 2023.
“A kowane wata, kilo giram 1 maras kashi na naman sa ya karu da kashi 1.12 bisa dari daga N2,418.91 da aka samu a watan Janairun 2023.”
Rahoton ya nuna cewa matsakaicin farashin shinkafa kilo 1 (na gida, ana siyar da sako) yana karuwa a duk shekara da kashi 19.30 daga N436.58 a watan Fabrairun 2022 zuwa N520.84 a watan Fabrairun 2023.
“A kowane wata, matsakaicin farashin wannan kayan ya karu da kashi 1.17 daga N514.83 a watan Janairun 2023.”
Rahoton ya kuma ce matsakaicin farashin tumatir kilo 1 a duk shekara, ya tashi da kashi 19.08 bisa dari daga N393.08 a watan Fabrairun 2022 zuwa N468.09 a watan Fabrairun 2023.
“Haka kuma, a kowane wata, kilogiram 1 na tumatir ya karu da kashi 0.22 cikin 100 a watan Fabrairun 2023.”
Hukumar NBS ta kuma ce matsakaicin farashin man kayan lambu guda daya ya tsaya kan N1,196.68 a watan Fabrairun 2023, wanda ya nuna karuwar kashi 25.91 cikin 100 daga N950.46 da aka samu a watan Fabrairun 2022.
