Connect with us

Labarai

Ganduje Ya Mayarwa Da Abba Gida Gida Martani

 

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya shaidawa zababben gwamnan, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, cewa shi ne ke kan mulki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga gargadin da Abba ya bayar tun farko.

Zababben gwamnan ya bukaci jama’a da su kaurace wa gine-ginen jama’a kuma su guji gine-gine a filayen gwamnati da makarantu da sauran wuraren taruwar jama’a.

Amma da yake magana ta bakin kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba, Ganduje ya bukaci Abba Yusuf da ya daina yin magana a hukumance domin gudun rudani a jihar.

Ya ce, “Ayyukan da zababben gwamnan ya yi zai kai ga haddasa cece kicee ta hanyar bayar da umarni kan wani lamari da ya shafi manufofin gwamnati yayin da mai ci bai cika wa’adinsa ba.”

Ganduje ya kara da cewa, dangane da batun rabon mukamai kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya tanada, ya ci gaba da zama gwamna da ikon zartarwa har zuwa ranar 29 ga watan Mayu, kuma yana da hakkin gudanar da ayyukansa bisa maslahar jama’a har zuwa jajiberen saukarsa.

“Har sai ya zama gwamna a ofishi a ranar 29 ga watan Mayu, ya ci gaba da zama zababben gwamna, kuma ba shi da ikon gwamna. Abin da kawai zai iya yi shi ne ya mayar da wasu ayyukan da magabacinsa ya yi a lokacin da ya hau kan karagar mulki idan har akwai kwararan dalilai na yin hakan.

“Sanarwar ta kara da cewa, babu wani zababben gwamnan da yake da ikon tsarin mulki ko doka na tantance alkiblar jihar har sai an rantsar da shi.

Ya kara da cewa a matsayinsa na gwamna, yana da gagarumin iko wajen rabon filayen, inda ya jaddada cewa kowace gwamnati ta yi irin wannan aiki, ciki har da gwamnatin da ta shude wadda zababben gwamna ya yi aiki a cikinta”.

Ya kuma bayyana cewa bisa ga bayanan da ake da su, gwamnatin da ta shude ta yi rabon filayen a wasu wuraren taruwar jama’a da zababben gwamnan ya ambata da suka hada da ganuwar birnin, tare da raba fili daga Kofar Nassarawa zuwa Kofar Mata; shaguna a filin Sallar Idi na kofar Mata da ke fuskantar gidan sinimar Orion da kuma daga Kofar Mata zuwa ‘Yan yashi daura da filin Idi da kuma daga Kofar Kabuga zuwa Kofar Famfo da ke fuskantar tsohon Campus na Jami’ar Bayero.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetgrandpashabetmarsbahismarsbahismarsbahistipobettipobetjojobetjojobet girişmarsbahisgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişjojobetjojobetgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahisjojobettipobetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet