Connect with us

Labarai

Gwamnatin Ganduje ta yi wa Abba Gida-Gida martani kan dakatar da gine-gine

Gwamnatin jihar Kano ta yi wa sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Engr Abba Kabir Yusuf martani bisa shawarar dakatar da gine-gine a filayen gwamnatin da hanyoyin ruwa.

Gwamnatin ta yi martanin ne ta cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Malam Muhammad Garba ya fitar da yammacin yau Juma’a.

Sanarwar ta ce, kamata ya yi gwamnan mai jiran gado ya yi haƙuri ya jira har zuwa lokacin da aka rantsar da shi tukunna ba wai yi wa gwamnati katsalandan ba.

Haka kuma sanarwar ta ce, irin wannan shawara za ta iya haddasa ruɗani ga al’umma.

Gwamnatin ta kuma ce, fitar da wannan sanarwa da a halin yanzu ba komai ba ce illa abunda za a iya kira da yin riga malam masallaci.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, zai ci gaba da shugabancin Kano har zuwa ranar 29 ga watan Mayun bana kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Idan za a iya tunawa dai, a daren jiya Alhamis Abba Kabir Yusuf ta hannun babban sakatarensa na yaɗa labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da wata sanarwa a matsayin shawara ga masu yin gine-gine a filaye da wuraren gwamnati da su dakata da yin hakan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet